Sports
Barca da Sevilla: ‘Yan Barca za su kara da Sevilla a La Liga
Daga kabiru basiru fulatan
Sevilla ta ziyarci Barcelona, domin buga wasan mako na 30 a gasar La Liga da za su kece raini a Nou Camp ranar Lahadi.
Wasan farko da kungiyar da Xavi ke jan ragama za ta buga, bayan da kasashe suka kara ko dai a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya, ko kuma na sada zumunta.
Tuni Barcelona ta bayyana ‘yan wasa 22 da za su fuskanci wasan da zai yi zafi idan anjima.
Kungiyoyin sun kara a bana a gasar La Liga ranar 21 ga watan Disambar 2021, inda suka tashi 1-1.
Sevilla ce ta fara cin kwallo ta hannun Papu Gomez a minti na 32, daga baya Jules Kounde ya farkewa Barcelona a minti na 64.
Kungiyar Servilla tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 69, ita kuwa Barcelona mai maki 54 tana ta uku.
Real Madrid ce ta daya mi maki 69, wadda ta yi karawa 30, Atletico Madrid ce ta uku da maki 57, wadda ta yi fafatawa 30.
‘Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Pique, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembele, Dani Alves, Memphis, Adama, Braithwaite, Neto, Nico, Lenglet, Pedri, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Carevic da kuma Gavi.
‘Yan Barcelona da ba za su buga fafatawar ba sun hada da Sergino Dest, Ansu Fati, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti da ke jinya, yayin da Luuk De Jong ya kamu da cutar korona.
Sauran wasannin da za a buga a La Liga ranar Lahadi:
Athletic de Bilbaoda Elche
Real Betis da Osasuna
Granada da Rayo Vallecano
Valencia da Cadiz
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
