Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Mbappe, Salah, Eriksen, Abraham, Alexander Isak, Dembele
Daga yasir sani abdullahi
Tsofaffin kulob din da dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 30, wato Tottenham da Manchester United, na duba yiwuwar rattaba hannu kan kwantiragin dauko dan wasan a kyauta a kakar wasan bana bayan komawa sahun gaba a Brentford da ya yi. (Mail)
Manajan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce yana cike da farin-cikin yadda tattaunawarsu ke samun ci gaba da dan wasan gaba dan asalin Masar Mohamed Salah, mai shekara 29 ke gudana. (Liverpool Echo)
Ana yada jita-jitar cewa mai yiwuwa Liverpool ta dauko dan wasan gaba dan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23, daga Paris St-Germain a kakar wasan bana – idan Salah ya yanke shawarar barin kungiyar. (FourFourTwo)
Mbappe ya ce yana da zabin ci gaba da kasancewa a PSG, duk da cewa kwantiraginsa zai kare a kakar wasan nan. (Mirror)
Dan asalin Roma Tammy Abraham, mai shekara 24, ya tsegunta cewa mai yiwuwa zai koma Premier League. (Talksport, via Mail)
Matukar fatan Arsenal na rattaba hannu kan kwantiragi da mai kai hari dan Sweden Alexander Isak, dan shekara 22, bai yi nasara ba, hakan zai zamo gagarumin koma-baya idan Real Sociedad ta gagara kai gaci a gasar kwallon kafar Turai a kakar wasan bana. (Fichajes, via Football.London)
Dan wasan Jamus Serge Gnabry, mai shekara 26, na duba yiwuwar barin kungiyar Bayern Munich, a kakar wasan da muke ciki, gabanin sha’awar dauko dan wasan da kungiyoyin Real Madrid da Liverpool suka nuna. (Goal)
Har wa yau, Real Madrid na duba yiwuwar dauko dan wasan Belgium Belgium Eden Hazard mai shekara 31, a matsayin bashi domin fara kakar wasannin shekarar 2022-23. (AS
Barcelona ta shirya ganawa da wakilin Ousmane Dembele, kan sabon kwantiragi ga dan wasan Faransar mai shekara 24, wanda ya shirya tsaf domin zama dan wasa mai zaman kansa a kakar wasan bana.(Marca)
Manchester United ka iya sake rattaba hannu kan kwantiragin dan wasan tsakiya na Lazio da Sebia, Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27, domin maye gurbin dab wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba,mai shekara 29. (Corriere dello Sport, via Express)
An samu rabuwar kawuna a Manchester United kan yiwuwar rattaba hannun dauko sabon mai horas da ‘yan wasa na Ajax, Erik ten Hag a matsayin manajan kungiyar na dindindin. (MEN)
A lokacin da manajan Manchester United na yanzu, Juan Mata kwantiraginsa ya kare, tsohon dan wasan tsakiya na Sifaniya mai shekara 33, ba shi da wani shiri na yin murabus, ko shiga cikin ma’aikatan horaswa na United. (Fabrizio Romano, on Twitter)
Tottenham ta bude hanyar tattaunawa domin rattaba hannu kan dauko matashin dan wasa mai shekara 18, kuma mai kai hari Dane Scarlett. (Football Insider)
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
