Connect with us

Sports

Kasuwar yan kwallo: Makomar Raphinha,Skriniar, Zinchenko, Richarlison, Eriksen, de Jong da Pereira

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Chelsea na dab da kai karshen ciniki da dan wasan gaban Leeds United da Brazil Raphinha, duk da har yanzu Arsenal da Barcelona ma na nemansa.(Guardian)

Advertisement

Buba Marwa ya na neman tona asirin ‘Yan siyasa, NDLEA ta cafke masu harkar kwayoyi. 

Hakama (Mail) ta ruwaito cewa Chelsea ta mayar da hankali kan mai tsaron bayan Inter Milan da Slovakia Milan Skriniar, wanda PSG ma na nemansa.

Advertisement

(Get French Football News) ta ruwaito cewa tuni PSG ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Skriniar, da kuma Renato Sanchez na Lille.

A nan kuma (Mail) ta ruwaito cewa Chelsea na son daukar mai tsaron bayan Manchester City da Ukraine wato Oleksandr Zinchenko, duk da suna kan cinikin daukar Raheem Sterling daga Cityn.

Advertisement

Ita kuwa Manchester United na fatan sayen dan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie de Jong, kuma tana fatan hakan zai karfafa wa Christian Eriksen na Denmark ya je kungiyar. (Star)

Tottenham ta rike wuta kan dan wasan gaban Everton da Brazil Richarlison, duk da Toffees sun yi watsi da tayin fam miliyan 20 da dan wasan gefe Steven Bergwijn. (Telegraph – subscription required)

Advertisement

A nan kuma Crystal Palace ce ke dab da saye dan wasan tsakiyar Lens na Faransa Cheick Doucoure kan yuro miliyan 21. (Guardian)

An bai wa Fulham damar magana da dan wasan tsakiyar Brazil Andreas Pereira, bayan kai karshen ciniki da Manchester United duk da har yanzu yana zaman aro a Flamengo. (90 Min)

Advertisement

Southampton ta shiga jerin kungiyoyin da ke neman dan wasan Burnley Josh Brownhill. (90 Min)

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending