Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Pogba, Neves, Merino, Nunez, Bissouma, Cuadrado
Daga maryam bashir musa
Paul Pogba ya zama dan wasa na farko da a yanzu Paris St-Germain ta bai wa fifiko a cefanen da za ta yi. (Footmercato – in French)
Ita kuwa Arsenal dan wasan tsakiya na Wolves da Portugal Ruben Neves, mai shekara 25, take son saye. (Sky Sports)
Manchester City za ta jarraba sa’arta wajen zawarcin dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sifaniya, Mikel Merino, sai dai kudin na-gani-ina-so na tsohon dan wasan na Newcastle mai shekara 25 ya kai fam miliyan 50. (El Confidencial, via Manchester Evening News)
Haka kuma Pep Guardiola yana son karfafa takiyar kungiyar tasa da dan wasan River Plate Enzo Fernandez bayan da ya duba yanayin wasan dan Argentinar mai shekara 21, bayan da Manchester City ta sayi abokin wasansa shi ma dan Argentina Julian Alvarez, mai shekara 22, a watan Janairu. (Goal)
Kociyan Tottenham Antonio Conte yana son rike dan wasan tsakiya na Sweden Dejan Kulusevski wanda ke zaman aro daga Juventus, ya zama na dindindin. Dan wasan mai shekara 21 zai iya kaiwa fam miliyan 29, kari a kan yuro miliyan 10 da Spurs din suka biya na karbar aronsa tsawon wata 18. (Calciomercato – in Italian)
Shugaban gasar kwallon kwandon Amurka, NBA, Larry Tanenbaum tare da abokin hadin guiwar mallakar Facebook, Eduardo Saverin sun shiga hadakar kamfanin da daya daga cikin masu kungiyar Boston Celtics ke shugabanta, Stephen Pagliuca domin sayen Chelsea. (Sky News, via Mirror)
Dan wasan Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 22, zai bar Benfica a bazara a kan yuro miliyan 80. (Fabrizio Romano)
Duk da tsananin son da take yi wa Nunez, Arsenal ta yi kasa a jerin kungiyoyin da ke gaba-gaba wajen sayen dan wasan, inda ta zama a bayan Manchester United da Chelsea da PSG. (The Athletic – subscription required)
Ga alama Romelu Lukaku zai iya komawa San Siro yayin da tsohon shugaban Inter Milan Massimo Moratti ya ce kungiyar ta Serie A ta samu kanta cikin yanayi mai wuyar gaske kan yanke shawara tsakanin sayen dan wasan na Chelsea mai shekara 28 da kuma Paulo Dybala na Juventus, dan Argentina mai shekara 28 shi ma. (Rai, via Goal)
Dan bayan Besiktas Ridvan Yilmaz, mai shekara 20, ka iya hadewa da abokin wsansa a tawagar Turkiyya Caglar Soyuncu a Leicester, saboda kungiyar ta Premier na shirin taya dan wasan a kan fam miliyan 8.3, farashin da zai sa ta yi galaba a kan Torino da Stuttgart. (TGRT Haber – in Turkish)
Manchester United ta kara dagewa wajen sanya tsohon dan wasanta Robin van Persie a jerin masu taimaka wa sabon kocin da za ta dauka Erik ten Hag. (Mail)
Tottenham ka iya ribatar dakatawar da aka yi kan tattaunawar kwantiragin dan wasan Colombia Juan Cuadrado, ta janye dan wasan mai shekara 33 daga Juventus. (Team Talk)
Za a iya bayar da dan wasan Aston Villa dan Ingila Danny Ings, mai shekara 29, ga Brighton a musaya da dan wasan tsakiya na Mali Yves Bissouma mai shekara 25 a shirin da Steven Gerrard yake yi na rabuwa da wasu ‘yan wasan ya sake gina kungiyar ta Villa Park. (Mirror)
Newcastle na harin sayen dan wasan Brighton na Belgium Leandro Trossard, mai shekara 27. (Mail)
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
