Connect with us

Sports

DAYA DAGA CIKIN JARIRAN DA BUDURWAR CRISTIANO RONALDO TA HAIFA YA MUTU.

Published

on

Daga Khadija Abdullahi Mahmud.

 

 

Daya daga cikin jariran da Budurwar Cristiano Ronaldo watau Georgina Rodriguez ta haifa, ya mutu
Cristiano Ronaldo ya sanar da wannan a Instagram, ya bukaci mutane su ba su dama su wartsake

Cristiano Ronaldo ya fito shafinsa na Instagram ya bayyana cewa yaron da suka samu ya rasu a lokacin da Georgina Rodriguez ta je haihuwar tagwaye.

Goal.com ta ce an sa ran Rodriguez za ta haifi ‘yan biyu, amma sai aka tashi da mummunan labari a jiyan na cewa daya daga cikin jariran bai yi rai ba.

Advertisement

Sai dai Rodriguez mai shekara 28 tayi nasarar haihuwar macen da ke cikin ta. Kawo yanzu ba a san wani suna aka radawa jaririyar da aka samu ba.

Da yake bayani, ‘dan wasan na Manchester United ya bukaci a kyale su, su ji da makokin rashin, ya godewa malaman asibitin da suka karbi haihuwar.

‘Dan wasan gaban ya na da wasu yaran; Cristiano Jr da Mateo, sai kuma ‘yan mata Eva Da Alana.
Jawabin Ronaldo.
“Mu na masu tsananin takaicin bada sanarwar jaririnmu ya mutu. Mun ji duk zafin da iyaye za su iya ji.”
“Haihuwar jaririyar ne kurum ya ba mu kwari da farin ciki a yanzu. Mu na so mu godewa likitoci da malaman jinya da kwarewarsu da taimakonsu.”
-Cristiano Ronaldo

Rodriguez ta na samun miliyoyi duk wata
A baya kun ji yadda Budurwar da ake sa rai Cristiano Ronaldo zai aura watau Georgina Rodriguez ta ke wanke biyar, ta tsoma goma, alhali ta taso ne a marainiya.

Kusan duk wata, Miss Georgina Rodriguez ta na iya samun kudin da ya kai Naira miliyan 50 a asusun ta. Masoyin na ta ya ware mata kudi domin kula da yara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending