Sports
Manchester City vs Real Madrid: Yan Real Madrid da za su kara da Man City
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Real Madrid ta ziyarci Manchester City domin buga wasan Champions League zangon farko a daf da karshe da za su kara ranar Talata a Etihad.
City ce ke jan ragamar teburin gasar Premier League na bana da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu.
Real Madrid na bukatar maki daya, domin lashe kofin La Liga na kakar nan, duk da saura wasa hudu a karkare gasar, ta bai wa Barcelona tazarar maki 15.
Real Madrid ce kan gaba a yawan lashe Champions League 13 jumulla, ita kuwa City ba ta taba dauka ba.
Wannan shi ne karo na uku da City ta kai daf da karshe a gasa hudu baya, yayin da Real za ta buga wasa na 10 a daf da karshe a fafatawa 12 baya a Champions League.
Rabon da Real Madrid ta lashe Champions League tun kakar 2018, bayan da ta doke Liverpool a wasan karshe da ci 3-1.
Manchester City za ta ziyarci Real Madrid ranar 4 ga watan Mayu, domin buga wasa na biyu a Santiago Bernabeu.
Tuni dai Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da za su fuskanci City a wasan na hamayya.
Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco da Camavinga.
Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Bale, Vini Jr. da Rodrygo.
Wasannin da aka buga tsakanin City da Real:
Champions League Juma’a 7 ga watan Agustan 2020
- Man City 2 – 1 Real Madrid
Champions League Laraba 26 ga wwatan Fabrairun 2020
- Real Madrid 1 – 2 Man City
Champions League Laraba4 ga watan Mayun 2016
- Real Madrid 1 – 0 Man City
Champions League Talata 26 ga watan Afirilun 2016
- Man City 0 – 0 Real Madrid
Champions League Laraba 21 ga watan Nuwambar 2012
- Man City 1 – 1 Real Madrid
Champions League Talata 18 ga watan Satumbar 2012
- Real Madrid 3 – 2 Man City
