Connect with us

News

ANYI GUDUN GARA AN TADDA ZAGO

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

Kamar yadda kafofin watsala labarai har da BBC suka wallafa, ance Ministan Kudi Zainabu Shamsuna Ahmed ta maye gurbin dakataccen Babban Akanta Janar na Nigeria Ahmed Idris da wani dan kabilar Igbo mai suna Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku

Wacce rawa Gerrard zai iya takawa a wasansa da Man City don taimakawa Liverpool?

Hukumar EFCC tana binciken Ahmed Idris akan kudade sama da Naira biliyan 80 da ya karkatar da su saboda zalunci da rashin imani

Advertisement

To amma wani babban abin takaici, shima wannan Anamekwe Nwabuoku da Minister Zainabu ta kawo, yanzu haka akwai case dinsa a hukumar EFCC da jimawa ana bincikensa akan wasu makudan kudi da ya sace lokacin da yake rike da matsayin Director of Finance and Account (DFA) na ma’aikatar tsaron Kasa (Ministry of Defence) inda ya arzurta kansa da kudaden tsaro

Sannan ana zarginsa da cewa duk wata ma’aikatar tarayya da yayi aiki a gurin bangaren kudi sai yayi sata, kuma tuni hukumar EFCC ta kwace wasu daga cikin manyan kadarori da ya mallaka da kudaden sata a halin da ake ciki, kuma daga lokaci zuwa lokaci ana ganinsa yana zuwa babban ofishin hukumar EFCC akan binciken da ake masa

To ya akayi Ministan Kudi ta dauko irin wannan mutumi da hukumar EFCC take bincike ya bashi wannan matsayi?

Kin dakatar da wanda ake zargin barawo ne, kin dauko wanda aka tabbatar barawo ne, shin a ina matsalar take?

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending