Connect with us

News

Shugaba Buhari Ga Najeriya: Ba Zan Huta Ba Har Sai An Samu Zaman Lafiya a Kasar Nan.

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

 

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Buhari ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 58 da kafa rundunar sojojin saman Najeriya a nan Kano.

Advertisement

TAKARAR SHUGABAN ƘASA 2023: Mutum biyar kaɗai ke da gaske a cikin APC, sauran ‘yan rakiyar amarya ne -Gwamna Fayemi

Shugaban ya ce zuba jarin da gwamnatinsa ta yi a rundunar sojin sama ya taimaka wajen karya lagwon ‘yan ta’adda a kasar nan.

Ya yi alkawarin cewa, zai ci gaba da bai wa sojin sama goyon baya da ya dace a yaki da rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta.

Ya kuma ce gwamnatin sa baza ta gushe ba, har sai ta samar da ingantaccen tsaro a fadin kasar nan.

Kazalika Shugaba Muhammadu Buhari ya sadu da iyalan da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar da aka samu a unguwar Sabon Gari a makon da ya gabata.

Shugaban ya jajanta wa iyalan mutanen da wannan hatsari ya rutsa da su da Mai Martaba Sarkin Kano da kuma gwamna kan wannan lamari.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending