Connect with us

News

Kada Ku Yadda Ku Bari Barayi Masu Satar Kuɗin Talakawa Su Ci Banza -Buhari Ya Gargaɗi Ɓangaren Shari’a

Published

on

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace duk wata shari’ar rashawar da aka samu matsala a wurin ayyukanta saboda wasu uzurori, alama ce ta tambaya dangane da jajircewar ma’aikatan shari’ar kasar nan wurin yaki da rashawa.

Kisan da ake yi wa ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya ya isa haka- -CNG

Ya kara da cewa “kada a dagawa duk wani da aka kama da rashawa, ko zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da kuma duk wani laifi na kudi kafa daga fuskantar fushin hukuma.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha yayi kira ga ma’aikatan shari’a su yi kokarin toshe duk wasu gurabun sharia da masu laifukan cikin jama’a su ke boyewa.

Daga Karshe yayi jan hankalin kada shari’a ta tsaya a matsayin ‘yar kallo yayin da masu laifi su ke amfani da damar wurin tserewa da dukiyoyinmu, su kara karfi sannan su bai wa wasu kwarin-gwiwar shiga harkar rashawa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending