Sports
‘Yan Real Madrid da za su kara da Liverpool a Champions League
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Liverpool da Real Madrid za su buga wasan karshe a Champions League a birnin Paris din Faransa ranar Asabar.
Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Manchester City a daf da karshe, ita kuwa Liverpool nasara ta yi a kan Villareal.
Kungiyar Anfield ta yi harin lashe kofi hudu a bana, sai dai ta rasa na Premier League, bayan da Manchester City ta dauki na kakar nan a ranar karshe wato 22 ga watan Mayu.
City ta ci kofin Premier League na shida da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool, wadda ta dauki FA Cup da League Cup.
Real Madrid ita ce ta lashe La Liga na kakar nan, kuma na 35 jumulla, kuma ci Champions League 13 – 1955-56, 1956-57, 1957-58, 1958-59, 1959-60, 1965-66, 1997-98, 1999-2000, 2001-02, 2013-14, 2015-16, 2016-17, 2017-18.
Ita kuwa Liverpool tana da guda shida – 1976-77, 1977-78, 1980-81, 1983-84, 2004-05, 2018-19.
Wannan shi ne wasa na tara da za a fafata tsakanin Liverpool da Real Madrid, inda kungiyar Santiago Bernabeu ta yi nasara a hudu, ita kuwa ta Anfield ta ci uku, suka yi canjaras daya.
Ga tarihin jerin haduwa tsakanoin kungiyoyin:
Kakar 2020/2021
Champions League Laraba 14 ga watan Afirilu
Liverpool0 – 0Real Madrid
Champions League Talata 6 ga watan Afirilu
Real Madrid3 – 1Liverpool
Kakar 2017/2018
Champions League wasan karshe Asabar 26 ga watan Mayu
Real Madrid3 – 1Liverpool
Kakar 2014/2015
Champions League Talata 4 ga watan Nuwamba
Real Madrid1 – 0Liverpool
Champions League Laraba 22 ga watan Oktoba
Liverpool0 – 3Real Madrid
Kakar 2008/2009
Champions League Talata 10 ga watan Mayu
Liverpool4 – 0Real Madrid
Champions League Laraba 25 ga watan Fabrairu
Real Madrid0 – 1Liverpool
Kakar 1980/1981
European Cup Laraba 27 ga watan Mayu
Liverpool1 – 0Real Madrid
‘Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga Courtois, Lunin, Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo, F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.
