Connect with us

Sports

Karim Benzema ne gwarzon Champions League na bana

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

An bayyana dan wasan Real Madrid, Karim Benzema a matakin gwarzon Champions League na kakar 2021/22.

Dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 34, ya lashe kofin Zakarun Turai na biyar kenan, bayan da Real ta doke Liverpool 1-0 ranar Asabar a Faransa.

Ya kuma ci kwallo 15 a karawa 12 a Champions League a bana, wanda ke kan gaba a takarar kyautar Ballon d’Or ta kakar nan.

Shi kuwa Vinicius Jr. wanda ya ci Liverpool kwallon, an bayyana shi a matakin matashin da ba kamarsa a babbar gasar Zakarun Turai ta bana.

Mai sekara 21 ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da shida aka zura a raga a kakar ta 2021/22.

Advertisement

NECO Ta Kara Wa’adin Rajistar Jarabawar 2022

‘Yan wasa biyu suna daga cikin 11 da suka fi bajinta a Champions League har da Luka Modric da mai tsaron raga, Thibaut Courtois, wanda shi ne yafi taka rawar gani a ranar Asabar.

Liverpool wadda ta yi rashin nasara tana da ‘yan kwallo hudu daga 11 fitattu a gasar bana da suka hada da Trent Alexander-Arnold da Virgil van Dijk da Andy Robertson da kuma Fabinho.

Sauran ‘yan wasa 11 da ba kamarsu a Champions League a kakar nan sun hada da dan kwallon Paris St-Germain, Kylian Mbappe da na Manchester City, Kevin de Bruyne da kuma Antonio Rudiger na Chelsea.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending