Connect with us

News

Dan jarida Jamal khashoge an sanyawa wani titi suna

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

An sanyawa Wani titi suna dake kusa da affishin jakadancin saudiyya a Amurka da sunan Dan jaridan da akayiwa kisan gilla Jamal khashoge

BBC Hausa ta rawaito cewa ansanya sunan Jamal khashoge ne Dan tunawa da irin kisan da kasar saudiyya tayi Masa

An sauya suna titin da ke gaban ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Washington DC zuwa sunan Jamal Khashoggi, wanda wasu jami’an tsaron cikin gida na Saudiyya suka yi wa kisan gilla, lamarin da ya gigita duniya.

Karamar hukumar da yankin ke ciki ta sauya sunan titin zuwa Jamal Khashoggi Way domin ta tabbatar da ba a manta da marigayin ba, ko a “yi kokarin boye tarihin rayuwarsa”.

Hukumomin tsaron Amurka sun yanke hukunci cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ya byar da umarnin kisan Jamal Khashoggi. Sai dai ya musanta aikata laifin.

Advertisement

A watan gobe ake sa ran zai tattauna da shugaban Amurka Joe Biden.

Titin Jamal Khashoggi Way ba shi ne titi na farko da ke gaban wani ofishin jakadanci da aka sauya sunansa zuwa na wani mai adawa da gwamantin kasarsa ba.

A shekarar 2018, majalisar karamar hukumar yankin ta sauya sunan titin da ke gaban ofishin jakadancin Rasha zuwa sunan wani dan adawa da aka harbe a wajen Fadar Kremlin a 2015. Sunan dan adawa Oris nemstov

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending