Connect with us

News

Martanin da ya biyo bayan yunƙurin Ganduje na karɓo bashin biliyan 10

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, mazauna jihar da wajenta na mayar da martani game da yunƙurin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na karɓo bashin naira biliyan 10 don inganta harkokin tsaro a jihar.

A ranar Laraba ne Majalisar Dokokin Kano ta amince da buƙatar gwamnatin jihar ta ciyo bashin don sayen kayayyakin inganta tsaro da suka haɗa da kamar kyamarar CCTV.

“Daga cikin abubuwan da za a saya har da kyamarar tsaro ta CCTV da kuma gina ɗakunan ɗaukar bayanai ta yadda jami’an tsaro za su gudanar da ayyukansu cikin nasara,” kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye na Majalisa Labaran Abdu Madari ya shaida wa BBC Hausa.

Cikin martanin da suka yi game da ciyo bashin, ƙungiyoyin farar-hula a Kano sun yi zargin cewa a baya ma an karɓi irin wannan bashin da sunan inganta harkar ilimi, da samar da manyan motocin sufuri amma ba a gani a ƙasa ba.

Sai dai magoya bayan gwamnatin Ganduje na kare matakin da cewa “kafin ku zargi Ganduje, ga ɗaya daga cikin gadojin da ya gina a Kano kuma ba ta cikin ukun farko na ire-irenta”, a cewar wani mai suna Mohammed Shehu a shafinsa na Facebook.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending