News
Za mu murƙushe masu yi wa tsaron Najeriya zagon-ƙasa – Buhari
Daga Muhammad Muhammad Ibrahim
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shaida cewa masu daukar doka a hannusu, mallakar makamai ta haramtacciyar hanya, da kuma ribauta daga jefa tsoro da matsalolin tsaro za su ɗanɗana kudarsu.
Shugaban na waɗannan kalamai ne a garin Wudil na jihar Kano, a bikin yaye ɗalibai ‘yan sanda da ya halarta.
Buhari ya ce gwamnatinsa, za ta ci gaba da yaƙi da munanan aƙidu da miyagun mutane, yana mai jan hankali ‘yan sanda kan mayar da hankali a ayyukansu.
Sannan ya jadada bukatar samar da ci gaba a fasaha ko kariya daga hare-haren intanet, sannan ya ce za a tarwatsa maƙiyan kasa.
Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
