Connect with us

News

Ko wane ne zai yi wa APC takarar mataimaki?

Published

on

Dag Muhamad Muhammad Zahraddin

Sa’o’i ƙalilan ne suka rage wa jam’iyyun siyasa a Najeriya don miƙa sunayen ‘yan takararsu na shugaban ƙasa da mataimakansu ga Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa.

Jam’iyyu ƙalilan ne zuwa yanzu suka bayyana sunayen mataimakan ‘yan takararsu na shugaban ƙasa da suka fitar, yayin da mafi yawa ke ci gaba da nuƙu-nuƙu.

Tuni dai babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta sanar da mutumin da zai yi wa ɗan takararta Atiku Abubakar, mataimaki.

Sannan ana dakon jam’iyyar mai mulki ta APC, da sauran jam’iyyun da suka shirya shiga a fafata da su.

Masu sharhi dai na cewa muhimmancin mataimaki a siyasar Najeriya, na iya kambamawa ko ruguza tagomashin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending