News
Ba zamu zauna mu zuba ido kana kassara jihar Kano ba, sakon NNPP ga Ganduje akan bashin CCTV
Daga Kabiru basiru fulatan
Jam’iyyar NNPP tace ba zata zauna ta zuba idanu gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, na kassara jihar Kano ba, musamman yunkurinsa a wannan lokaci na karbo bashin kudi Naira Biliyan 10 daga bankin Access, domin saka Kyamarorin sirri a jihar, kamata yayi Ganduje ya sauke Farilla kafin ya tunkari Nafila, a cewar jam’iyyar.
Jawabin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aikewa manema labarai, ciki harda Nasara Radio, mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar ta NNPP na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, inda sanarwar tace, Ganduje yana amfani da kujerarsa wajen kassara goben al’ummar Kano da ‘ya’yansu, domin hatta kudin makaranta ya gagara biya, dalilin haka yara da dama sun hakura da karatu.
Sanarwar ta kara da cewa, ba daidai bane Ganduje yayi watsi da abinda yafi damun al’umma ba, kamar karancin ruwan sha da sauransu, ya tafi aikin da tuntuni tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya samar da irin wadannan Kyamarori a lokacin mulkinsa, kuma kowa ya san cewar gwamnatin Ganduje ba zata iya rike ragamar kula da wadannan Kyamarori ba.
“Jam’iyyar NNPP na kira ga ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, su daina bawa Ganduje damar karbo irin wadannan bashi, ya kamata yan majalisa su dinga duba bukatun al’umma kafin aiwatar da irin wannan, domin muna sane da yadda a baya ya karbo bashin Biliyan 15 na harkar ilimi, amma an karkatar da kudin, an kai matakin da jarabawar daliban aji 6 na firamare (Common Entrance) ta gagara a Kano.
“Mu muna zargin ma zai karbo bashin ne domin maye gurbin abinda aka rasa a yayin zabukan fidda gwani da suka gabata, saboda haka shi kansa bankin Access da sauran bakuna muna kiransu da su kiyayi bawa Ganduje bashi.”
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
