Wata mata mai shekara 90 mai suna Ashake Atogi ta kaɗa ƙuri’a a zaɓen Jihar Ekiti, kamar yadda hukumar INEC ta sanar a shafinta na Twitter.
Ta kaɗa ƙuri’ar ne a rumfa mai lamba ɗaya da ke Irepodun/Ifelodun.

Daga.MuhammadMuhammad Zahraddin
Wata mata mai shekara 90 mai suna Ashake Atogi ta kaɗa ƙuri’a a zaɓen Jihar Ekiti, kamar yadda hukumar INEC ta sanar a shafinta na Twitter.
Ta kaɗa ƙuri’ar ne a rumfa mai lamba ɗaya da ke Irepodun/Ifelodun.


Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Ekiti ta bayyana cewa zaɓen da ake gudanarwa a jihar zuwa yanzu babu wasu rahotanni da ke nuna cewa an samu tashin hankali.
Mataimakin shugaban sufeton ƴan sandan Najeriya DIG Johnson Kokumo wanda shi ne ke jagorantar ɓangaren tsaro a zaɓen a jihar shi ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga jama’a a Ado-Ekiti.


Wasu daga cikin masu zaɓe a Ekiti sun harzuƙa kan wasu abubuwan da suke gani da ba su gane kansu ba.
Masu zaɓen waɗanda akasarinsu mata ne sun yi zargin cewa ana sayen ƙuri’a.
Wasu mata da ke rumfar zaɓe mai lamba 9 da 16 a mazaɓa ta 11 da ke Oke-ori omi sun ce suna so su yi zaɓe ne kawai ba sai an ba su kuɗi ba.
“Su tafi da kuɗinsu. Ba mu so mu yi zabe saboda tukunyar miya ɗaya. “Suna biyan wasu N2,500 wasu kuma suna biyan 2,000,” in ji ɗaya daga cikin masu zaɓen.
Wasu daga cikin wakilan jam’iyyu sun koka kan cewa akwai wata jam’iyya da ke raba kuɗi kuma sun ƙi su ba waɗanda suka ƙi zaɓarsu kuɗin.
“Muna so INEC ta turo sojoji waɗannan rumfunan zaben. Su kaɗai za su iya hana wannan sayen ƙuri’ar,” in ji ɗaya daga cikin masu zaɓen.

Ana dai ci gaba da gudanar da zaɓe a Jihar Ekiti domin zaɓen gwamnan da zai maye gurbin Kayode Fayemi.
Hukumar INEC dai ta ce za a kammala kaɗa ƙuri’a da misalin 2:30 na rana.
Zuwa yanzu dai babu wata matsala inda rahotanni ke cewa ana gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana.



Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya kaɗa ƙuri’arsa a zaben da ake gudanarwa a jihar.
Mista Fayemi ya kaɗa ƙuri’ar tasa ne a rumfar zaɓensa da ke mazaɓa ta 11 a Isan-Ekiti. Ita ma matarsa ta kaɗa ƙuri’arta ba tare da wata matsala ba.
Mista Fayemi ya yi kira ga waɗanda suka cancanci jefa ƙuri’a da su yi abin da ya dace wurin zaɓen wanda suke so ya jagorance su.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin ganin an gudanar da zaɓen lafiya an kuma gama lafiya.
Gwamna Fayemi dai zai miƙa ragamar jagorancin Jihar Ekiti ga duk wanda ya yi nasara a wannan zaɓe.
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana