News
Wuta ta ja ɓarawo ya rasu yayin sata a taransifoma — Ƴan sanda
Daga kabiru basiru fulatan
Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta tabbatar da cewa da a ke zargi ɓarawon kayan taransifoma ne ya rasa ransa bayan da wuta ta ja shi a kauyen Amoji-Ukwu da ke Ƙaramar Hukumar Obingwa a jihar.
Na tsallake rijiya da baya a wajen yaran garuna
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ɓarawo ne da har ya yanke wayoyi biyu a jikin na’urar ta taransifoma da sanyin safiyar Juma’a.
Ogbonna ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Asabar a Aba.
Wani mazaunin kauyen Amoji-Ukwu, Chinenye Agomuo, ya bayyana cewa, an ji ƙarar fashewar wani abu a ranar Juma’a, kuma lamarin ya faru ne lokacin da wani mutum ya yanke wayoyi a jikin taransfoma.
“A safiyar Juma’a, da misalin karfe 4:00 na safe, mun ji karar fashewar wani abu da ake zargin na’urar taranfoma ce.
“Bayan fashewar, na fara samun kiran waya daga dan uwana da ke zaune kusa da tiransfomar, yana neman in zo wajen da abin ya faru.
“Ya ce wani ne ya hau taransfoma sai wutar lantarki ta kama shi.
“Lokacin da muka isa wurin, sai muka ga ashe matashi ne.
Agomuo ya ce “Ya haura cikin taransifomar ne don yanke wayoyi, inda a hakan ne sai wutar ta kama shi ya mutu,” in ji shi.
Ya ce al’ummar yankin sun kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda na Gabashin Ngwa.
Agomuo ya ce an ajiye gawar wanda ake zargin a mutuware tare da taimakon ‘yan sanda.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
