Connect with us

News

Za mu kwashe dukkan alhazan Najeriya da suka rage – NAHCON

Published

on

Shugaban hukumar NAHCON

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Hukumar alhazai ta Najeriya ta jaddada cewa tana da ƙwarin gwiwar kwashe dukkan maniyyatan da suka rage a ƙasa yayin da ake shirin rufe jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a daren yau Lahadi.

Advertisement

Wuta ta ja ɓarawo ya rasu yayin sata a taransifoma — Ƴan sanda

Zuwa yanzu maniyyata fiye da 18,000 ne suke jiran a kai su Saudiyyar, yayin da hukumar ta NAHCON ta kwashe 25,361 kawai daga cikin fiye da 43,000 na alhazan Najeriya.

 

Daga ƙarfe 12:00 na daren yau Lahadi wa’adin rufe jigilar maniyyata zai cika, kodayake wasu kamfanonin sufurin jirage sun samu ƙarin awanni na ci gaba da aikin.

 

Yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Lahadi, NAHCON ta ce tana da ƙwarin gwiwar kwashe maniyyatan da suka rage zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending