Connect with us

Politics

2023: Kwankwaso ya fi duk ƴan takarar shugaban ƙasar nan — Sheikh Aminuddeen

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Daawah a Kano, Sheikh Muhammad Aminuddeen, ya buƙaci ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya ƙara himma a kan takarar sa ta neman shugabancin ƙasar nan.

Advertisement

 

Babban limamin, wanda ɗan marigayi shahararren malamin addinin Musuluncin nan ne a Kano, Sheikh Aminuddeen Abubakar, wanda ya kafa ya kafa Gidauniyar Daawah Group of Nigeria.

Advertisement

Jam’iyyar NNPP Tayi Allah-Wadai Da Korar Malaman Makaranta Sama Da Dubu Biyu A Jihar Kaduna

Da ya ke gabatar da huɗuba bayan an sallar idi ga dubban masallata da suka hada da Kwankwaso a yau Asabar, limamin ya ce tsohon gwamnan jihar Kano “yana da dukkan kyawawan halaye da zai jagoranci Najeriya kuma ya fi sauran ƴan takarar shugaban kasa na APC da PDP.”

Advertisement

 

Ya lura cewa MKwankwaso “yana matukar son ci gaban Najeriya”.

Advertisement

 

Shehin Malamin ya kara da cewa tsohon ministan tsaron abokin mahaifinsa ne, marigayi Sheikh Aminuddeen wanda ya rasu a shekarar 2015.

Advertisement

 

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da Nijeriya daga kalubalen tsaro da ake fama da shi, Ya kuma yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari jagora ya jagoranci kasar nan cikin nasara.

Advertisement

 

Sallar ta kuma samu halartar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a Kano, Abba Kabir Yusuf da abokin takararsa Kwamared Aminu Abdussalam da sauran manyan baƙi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending