News
2023: Fintiri ya ajiye Crowther Seth ya ɗauki farfesa mace a matsayin abokiyar takara
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnan JIHAR Adamawa kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 a jihar, Ahmadu Fintiri, ya ɗauki Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin abokiysr takararsa.
Kotu Ta Umarci MTN Ya Biya Mawaki Diyyar N20m
Mrs Farauta ita ce shugabar jami’ar jihar Adamawa ADSU, Mubi.
Mai magana da yawun gwamnan, Solomon Kumangar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Alhamis a Yola.
Farauta dai ta fito daga Numan, a shiyyar kudancin jihar Adamawa.
A baya dai ta riƙe muƙamin shugabar hukumar kula da ilimin bai-ɗaya ta jihar Adamawa, ADSUBEB, sannan kuma ta riƙe kwamishinan ilimi.
Ta kasance malama a Jami’ar Modibbo Adama, MAU, Yola.
Farauta, wacce aka haifa a ranar 28 ga Nuwamba, 1965 a Numan, Kudancin Adamawa, tana da aure da ’ya’ya.
