Connect with us

News

Buhari Ya Nemi ‘Yan Najeriya Su Fallasa Maboyar ‘Yan Ta’adda

Published

on

Muhammadu Buhari

Daga khadija Abdullah muhmd 

 

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana barayin daji da sauran ‘yan ta’adda a matsayin masu izgilanci da za a yi maganin su, a lokacin da ya je Daura bikin babbar Salla.

Bayan kwanaki 103, an fito da wasu fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

Advertisement

Da ya ke amsa tambayar manema labarai a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya bayan Sallar idin babbar Salla, Shugaba Buhari ya bayyana takaici kan yadda wasu miyagu kan kai hari kan jama’a haka kawai don mugun nufi.

 

Haka kuma shugaban ya bukaci jama’a su rika fallasa labarin maboyar miyagun ga jami’an tsaro don a kamasu a hukuntasu.

 

Da aka tambaye shi ko me zai cewa ‘yan Najeriya kasancewar wannan ita ce shekararsa ta karshe da zai yi idin babbar Sallah a matsayin shugaban kasa, Shugaban a takaice ya ce “su zauna lafiya” sai ya kama hanya ya bar inda ‘yan jaridar su ke.

 

Advertisement

Shugaba Buhari yana komawa gida bayan kammala sallar Idi a Daura

A watan Fabrairun badi ne dai za a gudanar da babban zabe a Najeriya yayin da shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na karshe a ranar 29 ga watan Mayu na 2023.

 

Ziyarar shugaba Buhari Daura na zuwa ne biyo bayan harin da aka kai kan wata tawagar motocinsa da ke kan hanyar zuwa Daura a cikin makon nan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending