Connect with us

News

Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Gwamnatin Jigawa ta ce gidaje 1,300 ne guguwar ta lalata a Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa.

Advertisement

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya bayar da rahoton cewa, lamarin da ya faru a ranar Talata da daddare, ya yi ɓarna sosai.

Kotu Za Ta Saurari Shari’ar Halasta Wa Ganduje Karbo Bashin Naira Biliyan 10

Mataimaki na musamman ga Gwamna Muhammad Badaru kan ci gaban al’umma da taimakon jama’a, Hamza Muhammad, ya shaida wa NAN a yau Asabar cewa, sama da gidaje 1,300 ne ibtila’in guguwar ya afkawa, inda wasu su ka rushe gaba ɗaya, wasu kuma su ka lalace.

 

Muhammad ya ce guguwar ta kuma lalata wasu sassan babban asibitin yankin da matatar ruwa da kuma makarantu.

Advertisement

 

“Daga rahoton tantancewar da na samu jiya, baya ga wadannan, guguwar ta kuma lalata rufin babban asibitin Kafin Hausa na dakunan haihuwa da na gaggawa da na wasu makarantun yankin.

 

“Haka kuma ya sauke wasu tankunan ruwa na sama, da kuma ɗaya daga cikin antenar sadarwa a yankin,” in ji Muhammad.

 

Sai dai ya ƙara da cewa an kai marasa lafiya a ɗakin haihuwar lafiya zuwa wasu wuraren kiwon lafiya.

Advertisement

 

Mataimakin ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, SEMA da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, sun kasance a yankin tun a ranar Laraba, inda suka tantance irin barnar da bala’in ya yi.

 

Wannan a cewarsa, domin baiwa gwamnati da hukumomi damar sanin irin barnar da guguwar ta haddasa, da nufin shiga tsakani da kuma bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending