Connect with us

News

Matashiyar da ke bayar da hayar kayan biki a Kano

Published

on

Daga Maryam bashir musa 

 

 

 

 

Wata matashiya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bude shagon bayar da hayar kayan biki da mata ke sanyawa a lokutan bukukwansu.

Advertisement

 

BBC Hausa ta rawaito Habiba Yusha’u wacce akafi sani da Beebas Glam, ta ce ta fara sana’ar ce bayan fahimtar yadda mata ke kashe kudi wajen sayan kayan tufafi yayin bikinsu wanda kuma ba su bukatar shi bayan bikin.

Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa

“Idan akayi lakari a kasar Hausa kusan duk bikin da za a yi, za ka ga amarya ta saka tufafi wanda sau daya kawai ake daura shi domin idan ta saka shi bayan biki za’a rika mata kallon mahaukaciya”.

 

Habiba tsohuwar mai sana’ar kwalliya ce amma a yanzu tafi mayar da hankali ne wajen bayar da hayar kayan amare lokacin bikinsu.

Advertisement

 

Matashiyar ta ce akwai duk irin kayan da amarya ke bukata kuma cikin farashi mai sauki saboda ta fara sana’ar ce domin taimakawa talakawa da marayu tun da ita ma marainiya ce.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending