Connect with us

News

Yariman Saudiyya ya nemi haɗin kan kasar Iran

Published

on

Mohammed Bin Salman

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed Bin Salman ya yi kira ga ƙasar Iran da ta hada kai da ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yankin Larabawa, tare da daina tsoma baki a al’amuran da suka shafi harkokin cikin gida na ƙasashen.

Matashiyar da ke bayar da hayar kayan biki a Kano

Advertisement

Yariman ya yi wannan kira ranar Asabar yayin bikin bude taron ƙoli na ƙungiyar da ke gudana a birnin Jidda na kasar Saudiyya. Kamar yadda jaridar Saudi gazzet ta ruwaito.

 

Ƙasashe mambobin ƙungiyar shida tare da ƙasashen Masar, da Jordan da kuma Iran ne ke halartar taron.

 

A jawabin buɗe taro Yariman na Saudiyya ya ce ana buƙatar haɗin kai domin taimakawa wajen farfaɗo da tattalin arziki duniya, sannan kuma ya yi gargaɗin cewa rashin tsari mai kyau game da makamashi ka iya haifar da hauhawar farashi a kasuwannin duniya.

 

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending