A yau jama’ar Jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya za su gudanar da zaɓen gwamna a jihar.
Ƴan takara 15 ne ake sa ran za su fafata a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar.
Ƴan takarar sun haɗa da;
- AP: Akinade Akanmu Ogunbiyi
- AAC: Awojide Peter Segun
- ADP: Kehinde Munirudeen Olumuyiwa A Atanda
- APC: Adegboyega Isiaka Oyetola
- APM: Awoyemi Oluwatayo Lukuman
- APP: Adebayo Adeolu Elisha
- BP: Adeleke Adesoji Masilo Aderemi Adedapo
- LP: Yussuff Sulaimon Lasun
- NNPP: Rasaq Oyelami Saliu
- NRM: Abede Adetona Samuel
- PDP: Adeleke Ademola Jackson Nurudeen
- PRP: Ayowole Olubusuyi Adedeji
- SDP: Omigbodun Oyegoke Akinrinola
- YPP: Ademola Bayonle Adeseye
- ZLP: Adesuyi John Olufemi
An kirkiri jihar Osun karkashin mulkin soji na Ibrahim Babangida, daga tsohuwar jihar Oyo a ranar 27 ga watan Agustan 1991.
Isiaka Adeleke, dan uwa ga dan takarar jam’iyyar PDP ne ya fara zama gwamnan jihar a watan Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993, lokacin da gwamnatin mulkin soji karkashin Ibrahim Babangida ta rusa mukaman siyasa bayan soke zaben June 12