Connect with us

News

Yadda tsabagin Talauci yasa yan Nageriya Ke Neman Masu Sayen Kuri’unsu A Zaben Gwamnan Osun.

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

 

Masu kada kuri’a sun rika neman wanda zai sayi kuri’unsu a bainar jama’a a zaben Gwamnan Jihar Osun.

Advertisement

Wani rahoton hadin gwiwa na rabin yinin zaben da cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai da suka yi aikin sanya ido a kan zaben ne ya bayyana haka.

Zaben Shugaba Nagari Yana Samar Da Kyakkyawan Shugabanci Ga Al’umma

Tallar kuri’u a fili

“Rahotanni sun nuna mutane sun rika fitowa fili suna neman sayar da kuri’unsu.

“Abin da ya rika faruwa ke nan a rumfa ta 02 Mazaba ta 06 a Ƙaramar Hukumar Iwokan da kuma rumfa ta 03, mazaba mai lamba 03 a Karamar Hukumar Ife ta Kudu abin da ya faru ke nan.

“Haka abin yake a rumfa mai lamba 03 a mazaba ta 07 a Karamar Hukumar Ife ta Arewa,” a cewar rahoton mai dauke da sa hannun Cibiyar Kirkie-kirkire da Ci Gaban Aikin Jarida (CJID) da kuma Cibiyar Nazarin Bincike ta Duniya (ICIR).

Advertisement

Sauran wadanda suka sa hannu kan rahoton su ne kafofin watsa labarai na Premium Times, Daily Trust, Nairametrics da Orient Daily.

Rahoton ya kara da cewa, “An samu samu cinikin kuri’u ta yadda wakilan jam’iyyu ke ta rubuta sunayen mutanen da suka amince su sayar musu da kuri’unsu a kan wani wani farashi.

“Irin haka ta faru a rumfa mai lamba 10, mazaba ta 03 a Karamar Hukumar Ife ta Gabas da rumfa mai lamba 01 mazaba ta 04 a Karamar Hukumar Iwo.

“A rumfa ta 02 Mazaba ta 06 a Ƙaramar Hukumar Iwokan da rumfa ta 03, mazaba mai lamba 03 a Karamar Hukumar Ife ta Kudu abin da ya faru ke nan.

“Haka abin yake a rumfa mai lamba 03 a mazaba ta 07 a Karamar Hukumar Ife ta Arewa.”

Kawo yanzu a fara tattara sakamakon zaben matakin kananan hukumomi.

Advertisement

Zaben na Gwamnan Jihar Osun na ranar Asabar 16 ga watan Yuli, 2022, shi ne irinsa na bakwai a jihar tun bayan komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a 1999, ya gudana ne a fadin kananan hukumomi 30 na jihar.

Sauran abubuwan da suka wakana da rahoton ya bayyana sun hada da:

Horo da tura masu sanya ido

Tun kafin zaben, Cibiyar kirkire-kirkire da ci gaban aikin jarida (CJID) wadda a baya ake kira Premium Times Centre for Investigative Journalism (PTCIJ) ta kafa cibiyar nazarin zabukan da za ta sanya ido a kai.

A kan haka ne cibiyar ta horar da kuma tura masu sa ido 39 a dukkan kananan hukumomin jihar Osun domin bayar da rahotanni da bayanai kan irin wainar da ake toyawa a zaben.

Isowar kayan zabe

Advertisement

Tun da misalin karfe 7:00 na safe masu sanya idon suka hallara a rumfunan zabe da aka tura su a fadin jihar domin ganin isowar kaya da jami’an zabe da yadda ake tantance masu zabe da yadda ake kirga kuri’a har zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zaben.

Sun bayyana cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tura jami’ai da kayan aiki zuwa rumfunan zabe a fadin jihar a kan lokaci.

Zuwa karfe 7:30 na safe jami’an INEC sun isa sama da kashi 70 cikin n100 na rumfunan zaben jihar.

Bude rumfunan zabe

Sai dai duk da haka yawancin rumfunan zabe ba su fara aiki da wuri ba.

Zuwa karfe 12 na rana kashi 40 cikin 100 kawai na rumfunan zabe ne suka fara aiki a kan lokaci, ragowar 58.9 kuma suka fara a makare.

Advertisement

Na’urar tantance masu zabe

An yi amfani da na’urar tantance masu zabe ta BVAS a duk rumfunan zabe da wakilan namu suka ziyarta.

Amma na’urorin sun ba da matsala a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomi irin su Egbedore da Iwo da Oke Adan da sauransu.

Akwai kuma rahoton bacewar sunayen wadansu wadanda suka yi rajistar zabe a BVAS din.

An hana mutanen da hakan ta shafa jefa kuri’a a zaben, duk kuwa da cewa suna da katin zabe na dindindin.

Masu bukata ta musamman

Advertisement

An bi tanadin dokar zabe ta bangaren ba da fifiko wajen yin zabe ga tsofaffi da mata masu juna biyu da marasa lafiya da nakasassu a kananan hukumomin da aka ziyarta.

Sai dai kuma duk da haka, ba a yi musu tanadi da ya kamata ba, musamman ma nakasassu.

A wasu rumfunan zabe nakasassu da masu tafiya da sanduna ba sa iya shiga wurare masu mahimmanci saboda tudu da matakala.

Ya kamata a kara kula da bukatun nakasassu kamar yadda sashe na 25 na dokar zabe na 2022 ya tanada.

Cinikin kuri’u

An samu labarin cinikin kuri’u a rumfar zabe mai lamba 010, masana mai lamba 03, Karamar Hukumar Ife ta Gabas Rumfar zabe mai lamba 01, mazaba mai lamba 04, Karama Hukumar Iwo.

Advertisement

An kuma ga wakilan jam’iyya suna daukar sunayen masu kada kuri’a da suka amince su sayar da kuri’unsu kan wani farashi.

Hakazalika, an samu karin kararrakin cinikin kuri’u wasu mazabu na Kananan Iwokan da Ife ta Kudu da Ife ta Arewa LGA a yayin da masu kada kuri’a suka fito fili suna neman sayar da kuri’unsu.

Tashin hankali

Haka kuma an hatsaniya a wasu rumfunan zabe sakamakon rashin aikin BVAS da korafe-korafen yadda aka tafiyar da zaben.

Haka kuma ’yam daba sun haddasa tashe-tashen hankula a rumfa ta 002, mazaba ta 07 a karamar hukumar Orolu, d kuma a mazaba ta 05 a karamar hukumar Iwo LGA, inda wasu da ake zargin ’yan daba ne suka yi artabu da jami’an tsaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending