News
Zaben Osun: Masu Zanga-Zanga Sun Taru A Matattara Sakamako
Daga kabiru basiru fulatan
Rahotanni daga Osun sun ce wasu masu zanga-zanga sun yi wa ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Osogbo, babban birnin Jihar, tsinke.
A ofishin na INEC ne dai ake tattara sakamakon kananan hukumomi; a can ne kuma za a sanar da wanda ya lashe zaben.
Guguwa ta lalata gidaje da gine-gine 1,300 a Jigawa
An kwantar da Osinbajo a asibiti
Yadda mutane ke neman masu sayen kuri’unsu a zaben Gwamnan Osun
Hakan na faruwa a daidai lokacin da Babban Baturen Zabe na Jihar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, yake fara karbar kammalallaen sakamakon daga turawan zabe na kananan hukumomi.
Masu zanga-zangar dai sun ce sun taru ne don tabbatar da cewa ba a ayyana zaben a matsayin inconclusive (wato bai kammala) ba.
Sai dai wani jami’in INEC ya tabbatar da cewa zaben na Osun ba zai taba zama inconclusive ba domin tuni sakamakon kananan hukumomin jihar 30 ya isa hannun Hukumar.
Ko da yake an sanar da sakamakon zaben a wadansu kananan hukumomi, sai yanzu aka fara tattara su a matakin jiha.
Aminiya ta bayar da labarin cewa a Jihar ta Osun ne aka fara ayyana zabe da cewa bai kammala ba.
Jam’iyyu fiye da 10 ne dai suka yi takara, amma fafatawa ta fi zafi a tsakanin jam’iyyun APC da PDP.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
