Connect with us

News

Miji na ya gudu tare da budurwarsa, mata mai neman a raba aurenta ta faɗa wa kotu

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

A yau Talata ne wata kotu da ke Jos ta tsakiya ta amince da roƙon wata matar aure, Rhoda Jonathan da ke neman a raba aurenta bisa hujjar cewa mijinta, Dakogol ya gudu tare da budurwarsa.

Jonathan a takardar neman a raba auren nata, ta yi zargin cewa Dakogol na yawan zagin ta kuma ya kasa biyan bukatun iyalinsa.

Alkalan da suka jagoranci shari’ar, Sadiq Adamu da Hyacenth Dolnanan, a wajen amincewa da rokon da Jonathan ta gabatar, sun ce; “duk kokarin sulhunta ma’auratan ya ci tura”.

Alkalan sun umarci mai kara da wanda ake kara da su rabu da juna kawai.

Sai dai kotun ta umurci Dakogol da ya rika bayar da kuɗin rainon ‘ya’yansa duk wata.

Advertisement

Tun da fari, Jonathan ta roki kotu da ta raba aurensu, inda ta ce mijin nata da su ke tare tsawon shekaru 20, ya kasa kula da ‘ya’yansu uku.

“Kafin ya gudu, watanni hudu da suka gabata, muna yawan samun saɓani, har ta kai ga ya daina sauke hakkinsa a matsayin miji na .

“Na gaji kuma ina so in ci gaba da rayuwata,” in ji ta.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending