News
JAMI’AN TSARO SUN KAMA MOTA DAUKE DA BAMA-BAMAI A JIHAR KANO
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar ‘yan sanda a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu bama-bamai a cikin wata mota kirar Mercedes Benz da ke kan hanyar Chiranchi a unguwar Dorayi a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin makamai da alburusai da aka kwato tare da gabatar da ‘yan ta’adda tare da aka kama da laifuka daban-daban a jihar.
CP Dikko ya ce mutanensa da ke aikin bincike ne suka tare motar domin bincike, yayin da suka kan aikin binciken, wadanda ke cikin motar suka bude wuta kana suka tsere.
A cewar sa “Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef a yayin da jami’an leken asiri da ke sintiri a unguwar Chiranchi Dorayi Kano, a yayin gudanar da bincike sun kama wata mota kirar Mercedes Benz.
“Yayin da suke shirin tsayarwa da binciken motar, sai mutanen da ke cikinta suka bude wa ‘yan sandan wuta, inda jami’an ‘yan sandan suka yi artabu da ‘yan bindigar da suka gudu suka bar motar.”
A cewarsa, an gano wadannan abubuwan; bindigogin A47 guda uku dauke da mujallu cike da alburusai casa’in, harsashi goma sha hudu na AK47, hannu daban-daban guda uku da kuma abubuwan fashewa daban-daban (IEDs).
CP Dikko ya ce: “Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi tare kokarin kama ‘yan ta’addan.
A bangare guda, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan Yuli.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Dikko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu a ranar Alhamis a Kano.
Ya ce 42 daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne da laifin fashi da makami, tara kuma da laifin garkuwa da mutane, 16 da laifin damfara da kuma 27 masu satar motoci da masu satar babura uku.
