News
Hatsarin Mota: Mutum 30 Sun Kone Kurmus A Hanyar Zariya Zuwa Kano
DAGA KHADIJA ABDULLAHI MAHMUD
Akalla mutum 30 sun kone kurmus yayin da wasu fasinjoji 12 kuma suka sami raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Tashar Musa da ke kan hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Alhamis.
Da yake tabbatar da aukuwar hatsarin, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) shiyyar Zariya, Abdulhamid Yakasai, ya ce motoci guda uku; kirar Homa guda biyu da Golf guda daya hatsarin ya shafa.
Zargin kalaman ɓatanci: A canja alƙalin da ke yin shari’a ta — Abduljabbar
Ya alakanta hatsarin da gudun wuce kima da kuma kokarin wuce na gaba ba tare da la’akari a da wasu direbobi ke yi ba a lokacin da suke tuki.
Yakasai ya kuma ce suna kokarin gano daga inda motocin suka taso da kuma lambobinsu domin sanar da ‘yan uwansu.
Tuni dai aka kai wadanda suka sami raunuka Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya tare da gawarwakin guda 30.
DAILY TRUST
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
