News
Gwamnan Kano ya karrama zakaran gasar Kimiyya da kudi Naira milyan uku
Daga yasir sani Abdullahi
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da tallafawa daliban jihar don cimma muradan su.
Kwamishiniyar ilmi mai zurfi ta jiha Dakta Mariya Mahmoud Bunkure ce ta shaida hakan, yayin taron tallafawa wani dalibi da yayi fice a wata gasa ta kasa baki daya.
Dakta Bunkure na cewa matakin da Gwamnatin Kano ta dauka na karrama dalibin Siyudi Sani, da kudi har Naira milyan uku, da kuma daukar nauyin karatunsa har zuwa Digiri na uku, na zuwa ne bayan fice da dalibin yayi a gasar Kimiyya ta jihar Kano da ake fi sani da ‘Young Kano State Scientist Governors Award’, da hakan ya bashi damar tafiya zuwa gasar kasa ta ‘Young Nigerian Scientist Presidential Award’ a turance, wanda kuma har yayi na daya a bangaren nazarin ilmin halittu masu rai na ‘Biology’.
‘Shakka babu wannan dalibi ya fidda jihar Kano kunya, wanda a gefe guda Gwamnatin Kano ta ga dacewar karrama shi don kara masa kwarin gwiwa.
‘Bayan wannan gasa ne kuma ya samu nasara a jarrabar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB, inda ya samu maki 303, wanda hakan ya bashi damar samun gurbin karatu a bangaren koyon aikin likitanci dake jami’ar Bayero’, a cewar Dakta Mariya Mahmoud Bunkure.
Kwamishiniyar ilmin mai zurfi ta jihar Kano, ta kuma kara da cewa, kokarin Gwamna bai tsaya anan ba inda ya sanya dalibin Siyudi Sani a wani kundi don bashi kulawa ta musamman, a wani mataki na samar da irin wadannan dalibai masu kwazo a cikin jihar.
Da yake jawabi tun da fari, Kwamishinan matasa da wasanni Alhaji Kabiru Ado Lakwaya, yabawa kokarin dalibin Siwidi yayi, inda ya ce Gwamnatin tayi tsari mai kyau wajen karrama matasa da suka nuna kwazo a fannonin karatu daban-daban, da bangaren ilmin kimiyya da fasaha.
Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan da kammala taron karramawar, dalibin Siyudi Sani ya godewa iyayensa da suka kula da shi har ya kai ga wannan nasara, wanda ya ce maida hankali kan karatunsa ya taimaka masa gaya wajen cimma wannan nasara.
‘Ya zama wajibi gare ni na godewa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da Kwamishiniyar ilmi mai zurfi da duk sauran manyan ma’aikatan da suka tallafa wannan mafarki ya zama gaskiya, wand azan yi duk mai yiwuwa wajen ganin na kare wannan kambu dana samu a matakin kasa’, Siyudi Sani.
Yasir sani Abdullahi
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
