News
‘Yan bindiga sun hallaka ‘yan sanda biyar da farar-hula 12 a jihar Katsina
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu ‘yan bindiga sun hallaka ‘yan sanda 5 da wasu farar hula akalla 3 a yankin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina a Najeriya.
Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana can cikin wani yanayi na alhini a yankin karamar hukumar bayan harin da ‘yan bindigar suka kai a yammacin jiya Laraba.
Zargin kalaman ɓatanci: A canja alƙalin da ke yin shari’a ta — Abduljabbar
Kamar yadda wani mutumin yankin mai suna Shamsuddini, wanda ya rasa kawunsa a harin ya shaida wa BBC.
Haka kuma wasu rahotanni daga yankin karamar hukumar Faskari a jihar ta Katsina na cewa wasu hare-haren da ‘yan bindiga suka kai sun yi sanadin asarar rayuka akalla 9 cikin kwana biyu.
Shugaban karamar hukumar ta Faskari, Musa Ado Faskari, ya koka kan yadda hare-haren ‘yan bindigar ke dada munana a yankin nasa a ‘yan kwanakin nan.
Yayin da BBC ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan a jihar Katsinar, SP Gambo Isa, ya tabbatar da labarin harin da aka kai yankin na Kankara.
Kakakin ya jaddada cewa, rundunarsu tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro suna yin iya bakin kokari, don ganin sun murkushe wannan matsala ta tsaro a sassan jihar ta Katsina.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
