Connect with us

News

Kotu ta bayar da belin Babban Akantan Najeriya da aka dakatar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Babban Akantan Najeriya da aka dakatar, Idris Ahmed tare da sauran wadanda hukumar EFCC ke tuhuma.

Advertisement

Da yake bayar da belin a yayin zaman shari’arsu a yau, alkalin kotun Justice Adeyemi Ajayi ya umarci mutanen da kada su bar yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

A duk minti daya Aids na kashe mutum daya a duniya

Advertisement

Kuma idan har suna son fita daga yankin na Abuja to lalle sai sun nemi izinin kotun ko kuma a soke belinsu.

Kotun ta kuma zartar da cewa dole n esu kiyaye da sharudan belin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriyar EFCC ta gindaya.

Advertisement

Idris da sauran wadanda ake tuhuma sun gurfana a gaban kotu a bisa zargin sata da almundahana har 14 da suka kai na kudi naira biliyan 109.5

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending