Ƙasashen Najeriya da Nijar da Aljeriya sun saka hannu kan yarjejeniyar samar da bututun iskar gas ta cikin Sahara da zai dangana da nahiyar Turai.
Ministan Makamashi na Aljeriya Mohamed Arkab ya faɗa wa manema labarai bayan bikin cewa “ƙasashen uku za su ci gaba da tattaunawa don fara aikin gadangadan”.
Yada Bayanan ’Yan Ta’adda: Gwamnati Za Ta Kafa Wa BBC Da Trust TV Takunkumi
Bututun da zai ratsa ta Nijar kuma ya dangane da Aljeriya, zai dinga samar da ma’aunin cubic metres na gas biliyan ɗaya 30 zuwa nahiyar Turai.
Da ma dai tuni Turawan suke fafutikar neman maye gurbin gas ɗin Rasha sakamaon rikicin Rashar da Ukraine.
An yi ƙiyasin za a kashe dala biliyan 13 wajen shimfiɗa bututun mai tsawon kilomita 4,000.
Tun a 2009 aka fara tattaunawa kan ƙulla yarjejeniyar amma ba a yi nasara ba..
