Connect with us

News

Akasarin ‘yan Najeriya na rayuwa cikin fargaba – Rahoto na World Risks Poll

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Najeriya ta shiga sahun kasashen da lamuran tsaro ke ci gaba da tabarbarewa, yayin da shugaban kasar, Muhammadu Buhari ke ci gaba da ikirarin cewa an inganta tsaro a gwamnatinsa.

Kamfanonin mai na cin kazamar riba a kan talakawa – MDD

Sai dai wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa mafi yawan ‘yan Najeriya ba sa cikin kwanciyar hankali fiye da yadda aka kasance shekaru biyar da suka gabata.

 

 

Advertisement

Rahoton mai taken “World Risk Poll” wanda wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aiki don Isamar da zaman lafiya a duniya mai suna, Lloyd’s Register Foundation, ta gudanar ya nuna cewa uku cikin biyar na ‘yan Najeriya wato kashi 61 cikin 100 kenan, ba sa cikin kwanciyar hankali fiye da yadda suka samu a shekarun baya.

Kungiyar ta tattara bayanai daga mutane 125,000 a cikin kasashe 121 donyin nazarin abubuwan da mutane suka fuskanta da kuma fahimtar hadurran da aka saba fuskanta, daga annoba da sauyin yanayi zuwa hadurran da ke da alaka da aiki da makamantansu.

Dangane da bayanan da aka tattara a cikin 2021 Najeriya ce kasa ta hudu mafi yawan mutanen da suka bayar da rahoton rashin tsaro, inda ta biyo bayan kasashen Lebanon, Afghanistan, da Venezuela.

A kashi 61 cikin 100, wannan adadin ya karu da kashi 26 cikin 100 tun bayan nazari na kasa da kasa na karshe da aka yi a shekarar 2019, lokacin da kashi 35 cikin 100 na ‘yan Najeriya suka bayar da rahoton rashin tsaro.

Rahoton ya ce, yayin da cutar Covid-19ake ganin na iya taka rawa, said ai dalilan da suka haddasa wannan karuwar suna da nasaba da yadda kasar ke fuskantar yawaitar laifuka da tashe-tashen hankula a shekarar 2021 da suka hada da ta’addanci da garkuwa da mutane.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Advertisement

Wannan dai ya bayyana ne a cikin sakamakon da kungiyar ta fitar, inda cikin rabin mutum 1,000 da aka ji ra’ayoyin su, sun bayyana cewa ko dai sun san wani ko kuma, sun fuskanci mummunar illa daga munanan laifuka a cikin shekaru biyu da suka wuce. Wannan ya ninka adadin a shekarar 2019 inda wannan adadi ya kai kashi 22 cikin dari.

Sakamakon da aka samu daga Najeriya yana da matukar damuwa,” in ji Sarah Cumbers, Daraktar gidauniyar ta Lloyd.

Yankunan da suka rigaya suka fuskanci talauci da rashin zaman lafiya, dole ne gwamnatoci da sauran masu tsara manufofi su yi aiki tare da al’ummomi don tsara dabarun kare mutane daga cututtuka masu zuwa wanda kuma ke haifar da sauran hadarin da za su iya samun kansu a yanzu.

Sauran matsalolin tsaro da ‘yan Najeriya ke kokawa sosai akai, sun hada da hadurran da ke faruwa a tituna ko ababen hawa da kashi 59, tsananin gurbatar yanayi da kashi 49, da kuma wuraren aiki da kashi 37.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending