Connect with us

News

Birtaniya ta bai wa likitoci ‘yan Najeriya 266 lasisi cikin wata biyu

Published

on

 DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Babbar kungiyar kiwon lafiya da ke bayar da lasisi ta jajirce cewa rijistar likitoci a Birtaniya ta bada lasisi ga likitoci ‘yan Najeriya 266 a watan Yuni da Yuli na 2022, a cewar rahoton jaridar Punch.

Tasirin haka shi ne akalla likitoci ‘yan Najeriya uku ake bai wa lasisi a kowace rana duk da yunkurin gamnati na dakile ficewar likitoci da jami’an kiwon lafiya daga kasar.

Da ɗumi-ɗumi: Ganduje ya miƙa ragamar mulkin Jihar Kano ga Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna.

A halin yanzu akwai likitoci da suka samu horo a Najeriya 9,976 da ke aiki a Birtaniya.

Advertisement

Wannan adadi bai kunshi wasu likitoci ba wadanda ‘yan Najeriya ne amma ba su samu horo a Najeriyar ba, a cewar rahoton.

Yanzu haka Najeriya ce kasa ta uku da ta fi kowace yawan likitoci da ke aiki a Birtaniya – bayan Indiya da Pakistan.

Sai dai duk da haka kasar na fama da karancin likitoci.

Kungiyar likitoci ta Najeriya ta ce akwai likitoci 100,000 da suka yi rijista da ita.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending