Sports
Ten Hag ya fara jan ragamar Man United a Premier da kafar hagu
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Manchester United ta sha kashi a hannun Brighton da ci 2-1 a Old Trafford a wasan farko da fara Premier League ta bana.
Brighton ta fara cin kwallo ta hannun Pascal Gross saura minti 15 su yi hutu, sannan shi ne ya kara na biyu a minti tara tsakani.
Pascal Gross ya ci Manchester United kwallo shida a Premier League shi kadai – shi ne kan gaba dan wasan Brighton da ya ci Uniteed kwallaye da yawa a gasar.
United ta zara daya bayan da aka koma zagaye na biyu, bayan da Alexis Mac Allister ya ci gida, saura minti 22 a tashi daga wasan.
Karon farko da kungiyoyin suka buga wasan bude Premier League wato makon farko a tsakaninsu.
A kakar da ta wuce, Brighton ta doke United 4-0 ranar 7 ga watan Mayu, bayan da tun farko United ta ci Brighton 2-0 ranar 15 ga watan Fabrairun 2021.
A wasa 14 baya kan haduwar ranar Lahadi – Brighton ta yi rashin nasara a wasa 12 a Old Trafford har da kwasar kashi a karawa takwas a jere a gidan United.
Koci biyar ‘yan kasar Netherlands da suka fara jan ragamar wasan farko a Premier sun sha kashi, in banda Guus Hiddink a Chelsea da ta doke Aston Villa a Villa Park a Fabrairun 2009.
United ta dauki wasu sabbin ‘yan wasa don tunkarar kakar bana da ya hada da Tyrell Malacia daga Feyenoord da Christian Erksen, wanda yarjejeniyarsa ya kare a Brentford da kuma Lisandro Matinez daga Ajax.
