Connect with us

Sports

Real Madrid ta ci wasa na biyu a jere a La Liga bayan casa Celta

Published

on

Madrid

Daga Usman Abdullahi jibirin

Real Madrid ta hada maki shida a wasa na biyu a La Liga ta bana, bayan da ta je ta casa Celta Vigo 4-1 ranar Asabar.

Advertisement

Karim Benzema ne ya fara ci wa Real kwallo a bugun fenariti, mai masaukin baki ta farke ta hannun Iago Aspas, shima a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Modric ne ya ci wa Real na biyu daga yadi na 25, bayan da David Alaba ya bashi kwallo.

Advertisement

Daga nan dan wasan Croatia, mai shekara 36 ya bai wa Vinicius Jr kwallo shi kuma ya jefa a ragae Agustin Marchesin.

Federico Valverde ya kara na hudu a wasan da Real ta hada makinta uku.

Advertisement

Real ta kara samun bugun fenariti a karo na biyu, inda Eden Hazard, wanda ya shiga wasan daga baya ya buga amma mai tsaron raga Marchesin ya tare.

Tsohon dan kwallon Chelsea ya ci kwallo hudu a wasa 50 da ya yi wa Real Madrid a La Liga.

Advertisement

Kawo yanzu Real ta yi nasara a dukkan wasa uku da fara yi a kakar nan, inda ta doke Eintracht Frankfurt a Uefa Super Cup da Almeria a wasan farko a La Liga.

Modric – wanda magoya bayan Celta suka yi tafi – ya ci kwallo a kalla daya a lik a gasar Bosnia da Croatia da England da Sifaniya a kowacce kaka.

Advertisement

Kuma 19 daga kwallo 33 da ya zura a raga a La Liga daga wajen da’ira ta 18 ya ci.

Rabon da Carlo Ancelotti ya yi rashin nasara a wasan La Liga a kan kungiyar da ba daga cikin birnin Madrid ba, tun doke ta Barcelona ta yi a Janairun 2021.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending