Sports
Anthony Joshua ya sha kaye a hannun Usyk
Daga: Usman Abdullahi jibirin
A jiya Asabar ne dai Anthony Joshua, ɗan dambe, wanda ya ke d5an kasar Birtaniya da Najeriya a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ya zubar da hawaye bayan ya sha kaye a hannun Oleksandr Usyk, ɗan kasar Ukraine.
Usyk, a karawa ta biyu, ya doke Joshua ya kuma rike kambun IBO, IBF, WBA da WBO.
A taron manema labarai bayan fafatawar, Joshua ya zubar da hawaye, yayin da ya ke bayyana ɓacin ransa sakamakon kayen da ya sha a bayan fafatawar.
“Ba na jin komai, na damu sosai a cikin zuciyata, Lokacin da ka samu rashin nasara, ba za ka yi farin ciki ba, abin haushi ne kawai.
“Na so in yi nasara kuma na so in yi nasara sabo da ƴan Birtaniya saboda na san yadda suke so in fafata da Tyson Fury. Ban yi farin ciki da wasan nan ba saboda ban yi nasara ba.
“Na yaba da duk wadanda su ka kalli wasan nan a gida, ni mayaki ne, amma ba a cikin yanayi mai daɗi nake ba,” in ji shi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
