Lauyoyi a Ingila da Wales sun tsunduma yajin aikin makonni biyu, kan batun karin albashi da gwamnati ta ki amincewa da shi.
Kungiyar lauyoyin na bukatar a kara musu kudaden gudanar da aiki da kashi daya cikin hudu na albashinsu, sai dai ministar shari’ar Birtaniya Sarah Dines, ta kira matakin da rashin da’a.
Kano, Zamfara, Enugu sun sami sabbin CPs
Wata jami’a a Queens Counsel, Michelle Heeley, da ke taimakawa lauyoyi a Birtaniya, ta ce ba bu adalci a batun karin albashin.
Ta ce wannna abu ne da yawancin mambobinsu ke magana a kai, inda da an kara kashi 15 na albashin watakil da ba za a soki gwamnati ba.
Ta ce an akara kashi 15 a kan albashin ne kan shari’un da ba ma za a kamalla ba sai 30 ga watan Satumba.
