News
An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe.
Daga idirs Hussaini Nguru
Rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma’a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.
Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.
Majiyoyin sun ce an bindige shi ne har lahira yayin da sojojin suka tafi da motarsa, Honda Accord (Discussion Continues) kafin yan sanda suka kama su.
Yan sanda sun bayyana sunayen wadanda ake zargin Kakakin yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma ce sojojin biyu da aka kama sune, Lance Corporal John Gabriel da Lance Corporal Adamu Gideon na 241 Recce Battalion, Nguru, Jihar Yobe.
- Lauyoyi a Ingila sun tsunduma yajin aiki
- Yawan Dukan Mata da Maza Ke Yi Ya Sa Za A Soma Gwajin Miyagun Ƙwayoyi Kafin A Yi Aure – Buba Marwa
Ya ce an kai wadanda ake zargin biyu sashin binciken manyan laifuka na SCID da ke Damaturu don zurfafa bincike.
An birne shahararren malamin a ranar Asabar a garin Gashua ta Jihar Yobe yayin da dubban yan uwa, dalibai da abokansa ke zubar da hawaye.
Shima a nasa bangaren, Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya nuna baƙin-cikinsa da kisan da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin.
Gwamna Buni a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya ce wannan kisa abin takaici ne da alla-wadai, don haka za a binciki lamarin.
Mai Mala ya ce duk wanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci. Sannan ya miƙa ta’azziyarsa zuwa da iyalan marigayin da al’ummar karamar hukumar Bade da ilahirin jihar kan kisan Aisami.
Gwamnan ya bukaci a kwantar da hankali yayinda ake kan gudanar da bincike.
