News
Tankin ruwa ya kashe mutane 2 a Legas
Daga Kabiru Basiru Fulatan
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta tabbatar da faɗowar tankin ruwa a kan mutane biyu har su ka rasa rayukansu a Ladi Lak, Bariga jihar Legas a daren jiya Lahadi.
Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan shiyyar Kudu-maso-Yamma na NEMA, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN faruwar lamarin a yau Litinin a Legas.
An samu karuwar yaduwar cutar kyandar biri a Najeriya
Farinloye ya ce tankin ya faɗo ne daga wani bene mai hawa biyu har ya faɗo a kan wasu maza su biyu, babba da yaro, yayin da wasu manya uku suka samu raunuka.
Ya ce shugabannin al’umma na yankin Bariga ne suka kai waɗanda suka jikkata asibiti kafin isowar jami’an agajin gaggawa.
Ya ce lamarin ya faru ne a titin Adeleye, Ladi Lak, Bariga, wani yanki na Legas.
Daily Nigerian
Error: Contact form not found.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
