Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Farfesa Rufa’i Alkali, yace jam’iyyarsu tana matukar ganin girman Sanata Ibrahim Shekarau, amma ba zasu yarda a saka jam’iyyar cikin wani rikici na babu gaira babu dalili don zai fice daga jam’iyyar ba, kuma basu da matsala da duk matakin da ya dauka.
Alkali ya bayyana haka ne yau a jihar Lagos yayin ganawa da manema labarai, inda yace rashin mutum daya a siyasa asara ce, amma kuma hakan baya nufin rashin nasara, sai dai yasa a kara zage damtse, saboda haka suna kan tattaunawa da Shekarau domin ganin an shawo kan rashin fahimtar juna da ta shiga tsakani, ba shi kadai ba, duk wata matsala a kowacce jiha ana kokarin magance ta, domin tuni aka samar da kwamitin sasanci na jam’iyyar a kowanne mataki, inji shi.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, Sanata Shekarau yayi taron majalisar Shura a gidansa dake Mundabawa Kano, inda ya bayyana cewa ba’a cika masa alkawuran da akayi masa a jam’iyyar ba, saboda haka kuma a jira shi nan da kwanaki kadan domin jin matsayarsa.
