Connect with us

News

Yanzu-Yanzu: Ganduje zai samar da ƙarin jami’o’i guda biyu a Kano

Published

on

Ganduje

 

Daga: Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Gwamnati jihar kano ta yi alkawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin Kara bada damar inganta Ilimin matasa a jihar nan.

Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabin yayin buɗe taron makon matasa, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin duba akan matsalolin matasa da kuma lalubo hanyoyin da za’a magancesu.

An gudanar da taron ne a rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a yau Laraba.

Advertisement

A cewar Ganduje, tuni an tura sunayen Kwalejin Horas da Malamai ta Sa’adatu Rimi da kuma Kwalejin Koyar da Aikin noma ta Audu Bako da ke Danbatta ga hukumar da take kula da jami’o’i ta kasa (NUC) domin neman sahalewa.

Ya ce ya yi hakan ne domin ƙara baiwa matasa damar su ƙara karatu don inganta rayuwarsu da kuma cigaban jihar Kano baki ɗaya.

Idan wadannan jami’o’i suka tabbata Kano tana da jami’o’i guda 4 kenan mallakin gwamnatin jiha.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending