News
Atiku yayi watsi da bukatar Sule Lamido, ya tafi London rarrashin Wike
Daga: Muhammad Muhammad zahraddin
Bayan rahoton wata ganawa da akayi tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, acan birnin London, tuni wasu rahotanni suka nuna cewa shima dan takarar PDP, Atiku Abubakar, ya bazama zuwa London domin rarrashin Wike akan mara masa baya don kaiwa gaci a babban zaɓen shekarar 2023.
Tun bayan gudanar da zaɓen fidda gwani na dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta gudanar, wanda Atiku yayi nasara, Wike yaja baya a sha’anin jam’iyyar, ya kuma gana da manyan jagororin siyasar Nigeria daga jam’iyyu daban-daban.
Hakan na zuwa ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bukaci jam’iyyarsu ta PDP ta kyale Wike yayi duk abinda zaiyi, domin a cewarsa bai isa ya hana Atiku samun nasara a jihar Rivers ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
