Adadin mutanen da suka rasu a Pakistan sakamakon ambaliyar ruwa ya haura dubu ɗaya.
Hukumar kiyaye afkuwar bala’i da bayar da agajin gaggawa ta ƙasar, ta ce cikin sa’a 24, mutum ɗari da sha tara aka tabbatar da sun rasu.
NNPP za ta ƙwace mulki a hannun Zulum a zaɓen 2023, In ji Kwankwaso
Ko a jiya Asabar sai da Pakistan ɗin ta yi kira ga ƙasashen duniya da su kai mata ɗauki sakamakon wannan ambaliya da ta shafi miliyoyin mutane da raba dubbai da muhallansu.
Rahotanni na cewa akwai wurare da dama da suka zama tsibirai inda ake ci gaba da zabga ruwa a Pakistan ɗin.
Kusa da birnin Larkana, akwai dubban gidajen ƙasa da ruwa ya shanye, abin da za a iya hangowa daga nesa idan ana tunkarar gari kawai shi ne saman bishiyoyi.
Wuraren da kuma ruwan ke da sauƙi-sauƙi shi ne mutum zai iya hangen rufin gidajen mutane, inda ruwan ya shanye gaba ɗaya gine-gine.
