News
Har yanzu Sha’aban ne dan takararmu na gwamnan Kano ba Koguna ba — ADP
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Jam’iyyar ADP tace har yanzu Sha’aban Ibrahim Sharada ne wanda zaiyi mata takarar gwamnan Kano a kakar zaben shekarar 2023 mai zuwa, sakamakon janyewa da Nasiru Hassan Koguna yayi, kuma Sha’aban ya cika dukkan ka’idojin zama dan takara.
Jawabin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Rabiu Ahmad Bako, ya aikewa manema labarai, inda yace tabbas Koguna ya janyewa Sha’aban takararsa, kuma dukkan ka’idoji musamman na INEC an cika su, domin Sha’aban ya biya kudin fom da sauransu, kuma duk akwai shaidu.
“Muna kira ga dukkan magoya baya musamman yan jam’iyyar ADP, da sauran masu yi mana fatan alheri, akan cewa su kwantar da hankalinsu, domin muna fatan samun nasara.”
Ambaliya na ci gaba da laƙume rayuka a Pakistan
Sha’aban dai dan majalisar tarayya ne daga yankin karamar hukumar Birni a jihar Kano, wanda ya nemi takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC, amma kuma ya sha kaye a hannun Nasiru Yusuf Gawuna, kafin daga bisani ya fice daga jam’iyyar zuwa ADP ya samu tikitin takarar gwamna, bayan janye masa da ainihin dan takarar yayi.
To amma kuma tuni dan takara Koguna yace a dawo da Bako ya sha Kwai, domin kuwa an gaza cika masa alkawuran da aka dauka masa kafin ya janye, ciki harda maido masa da dukkan kudaden da ya kashe tun daga neman takara har zuwa fara shirye-shiryen yakin neman zaɓe, da kuma zama mataimakin dan takarar gwamna.
