News
Mutane da dama suna cigaba da rasa muhallinsu na zama a Nguru
Daga Idriss Hussain Nguru
Al, umma na cigaba da rasa muhallinsu na zama sakamakon ambaliyar ruwan sama da aka samu a yankin unguwar barma lamarin Ya zama barazana ga Al, ummar karshen kwalta
jaridar INDARANKA ta rawaito cewa har Zuwa wannan lokacin ba, asan adadin mutanan da abun Ya shafa ba, Ansamu asarar dukiyoyi da dama.

Yau tsawon sati uku kenan da al’umar
yankin suka fara barin gidajensu, haka zalika a halin yanzu wasu daga cikinsu sun samu gidajen aro, wasu Kuma na haya, wasu ko har yanzu basu ga tsuntsu basu ga tarko.

kawo yanzu babu wani agaji da suka samu a hukumance. Kuma har izuwa yanzu kullum gidajen rushewa suke daga gidajen kasa (laka) har da na zamani saboda ruwan yaci karfinsu.

Muna kara kira ga hukumomi da su taimaka wajan fitar da wannan ruwa zuwa inda ya dace domin barnar da yakeyi bazata misaltuba.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
