News
An kammala aikin ceto a wajen rushewar gini a Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
An kammala aikin ceto a wajen da wani bene mai hawa uku ya rushe a kasuwar beirut da ke Jihar Kano – inda gini ya danne mutane da dama
Jami’an agajin gaggawa sun ce mutum daya ya mutu a baraguzan gini yayin da bakwai kuma suka samu raunuka, inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin basu kulawa da ta dace.
Mutum hudu sun kamu da cutar kyandar biri a Katsina
Sai dai hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce daya daga cikin wadanda suka samu raunuka ya samu karaya kuma yana asibiti ana kula da shi.
Hukumar ta NEMA ta fadawa BBC cewa ta kammala aikin ceto zuwa yanzu kuma babu sauran mutane da ke karkashin baraguzan gini.
Benen wanda yake dauke da shaguna da dama ba a kammala gina shi ba kafin ya rushe a jiya Talata. Ba a dai san me ya haddasa rushewar ginin ba.
Ana yawaita samun rushewar gine-gine a biranen Najeriya da ke janyo asarar rayuka, inda sau da dama ake dora laifin hakan a kan rashin bin ka’idojin gini da mutane basa bi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
